(ABNA24.com) Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Vladimir Padrino ministan tsaron kasar ta Vemezuela yana fadar haka a wani jawabin da ya yi a tashar talabijin ta kasar a jiya Alhamis.
Vladimir Padrino ya kara da cewa sojojin da aka kama suna daga cikin wadanda aka shirya juyin mulki wa shugaban Madoro da su, juyin mulkin da bai sami nasara ba a cikin yan makonni da suka gabata.
A farkon wannan watan da muke ciki ne wasu sojoji, masu samun goyon bayan Amurka, wadanda kuma suka fito daga kasar Colombia suka yi kokarin kutsawa cikin kasar ta Venezuela ta arewacin kasar, amma sajojin kasar hanasu shiga, banda haka sun kashe mutane 8 daga cikinsu sannan suka kama tsoffin sojojin Amurkawa biyu da ransa.
A halin yanzu dai za’a gurfanar da sojojin Amurkan biyu wato Luke Denman da kuma Airan Berry a gaban kotu a kasar, tare da tuhumarsu da ayyukan ta’addanci da kuma shigo da makamai kasar ba tare da izini ba.
/129
16 Mayu 2020 - 06:38
Lambar labari: 1037262
Sojojin kasar Venezuela sun kama bijirarrun sojojin kasar 39 wadanda suke kokarin shiga kasar ta kan iyakarta da kasar Colombia.